Yan Najeriya 6 Da Aka Taɓa Zaɓa A Takarar Gwarzon Ɗan Kwallon Duniya Na Ballon d’Or

‘Yan Najeriya shida ne aka zaba a matsayin gwarzon dan kwallon duniya na Ballon d’Or.

Kanu Nwankwo ya zo na 11 a takarar matsayin gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya a shekarar 1996- wanda shine matsayi mafi girma na dan wasan Najeriya.

Finidi George ya kasance a matsayi na 21 a cikin 1995.

Victor Ikpeba ya kasance a matsayi na 32 a cikin 1997.

An zabi Daniel Amokachi a shekarar 1995 amma bai samu kuri’a ba.

An zabi Austin Okocha a shekarar 1995 da 1996 amma bai samu kuri’a ba sau biyu.

An zabi Sunday Oliseh a shekarar 1998 amma bai samu kuri’a ba.