Wasanni

Yadda Stankovic Ya Bugawa Ƙasashe 3 Daban-Daban Ƙwallo A Gasar Cin Kofin Duniya

Dejan Stankovic ne kawai dan wasan kwallon kafa da ya bugawa kasashe uku daban-daban ƙwallo a gasar cin kofin duniya.

A gasar cin kofin duniya da aka yi a kasar Faransa a shekarar 1998, ya wakilci kasar Yugoslavia.

Amma a shekara ta 2003, Yugoslavia ya zama tarihi- kuma Serbia da Montenegro sun kasance.

A gasar cin kofin duniya da aka yi a Jamus a shekara ta 2006, Stankovic ya jagoranci Serbia da Montenegro.

A shekara ta 2010, Serbia da Montenegro sun zama ƙasashe biyu masu cin gashin kansu- kuma Stankovic ya buga wa Serbia wasa.