Wasanni

Yadda Rikicin Ryan Giggs Da Kaka Ya Ƙare Bayan Kammala Wasa

Ryan Giggs – “Wata rana na yi wa Kaka keta muna ciki wasa sai yasa hannunsa a makogwarona yayi damka kuma muka yi fada anan wurin.

Bayan wasan na same shi yana jirana tare da Gattuso. Gattuso ya gaya mani cewa Kaka yana so ya nemi gafara amma ba zai iya yin magana Turanci ba, na gaya masa cewa babu matsala kuma babu damuwa.

Bayan Gattuso ya fassara abin da na gaya wa Kaka, yazo wurina ya rungume ni ya sake ba ni hakuri. Mun canza rigar mu, ba zan taba mantawa da wannan ranar ba, inji Ryan Giggs.