Yadda Ake Fitar Da Wanda Yayi Nasara A Wasa Da Ta Tashi 0-0 Kafin Shigo Da ‘Bugun Finareti’

Kafin gabatar da bugun daga kai sai mai tsaron raga (Finareti) a wasan kwallon kafa, sake buga wasan na daya daga cikin hanyoyin da aka saba amfani da su wajen tantance wanda ya yi nasara a wasan da aka tashi canjaras (0-0 ko 1-1).

An buga wasan karshe na gasar Euro 1968 tsakanin Italiya da Yugoslavia sau biyu- wasan farko ya tashi 1-1 yayin da Italiya ta sake samun nasara da ci 2-0 a wasa ta biyu.

An buga wasan karshe na AFCON 1974 tsakanin Zaire da Zambia sau biyu- wasan farko ya tashi 2-2 yayin da Zaire ya sake lashe gasar da ci 2-0 a bugu na biyu.