Yanda Aka Fitar Da Najeriya Daga Gasar Cin Kofin Duniya Ta 2010

A wasan rukuni-rukuni a gasar cin kofin duniya ta 2010, an bai wa dan wasan Najeriya Sani Kaita jan kati kai tsaye saboda keta da ya yiwa dan wasan kasar Greece Vasilis Torosidis.

Greece ta taso daga ci 1-0 a wasan zuwa ci 2-1. Magoya bayan Najeriya sun fusata matuka saboda sun yi imanin laifin da Kaita ya yiwa dan wasan Greece bai zama dole ba kuma hakan ya sa suka ci wasan.

An bayyana cewa Kaita ya samu barazanar kisa da dama kuma jami’an tsaro sun kasance suna bakin aikin kare shi.

Wannan shine karo na karshe da aka taba ganin shi sanye da rigar Super Eagles.