Kasuwanci

Wata Mata Ta Kusa Yin Tsirara A Banki Bayan Miliyan N4 A Asusun Ta Sun Bace

Wata mata ta kusa yin tsirara a dakin karbar baki na wani banki bayan da kudin da ke asusun ta ya bace sama ko kasa.

Matar ta ce ta na ajiye kudin ne a gidan ta, kuma ‘yan fashin ba su yi mata sata ba. Amma da ta yanke shawarar ajiye kudin a banki, an yi mata fashin ajiyar rayuwar ta.

A cikin wani faifan bidiyo da aka yada a yanar gizo, an ga matar tana yawo a cikin falon bankin a firgice, tana kuka tana neman kudin ta.