Victor Osimhen Ya Ba Wani Yaro Da Yayi Irin Shigar Shi Kyautar Naira Miliyan N2.5

Dan wasan Super Eagles, Victor Osimhen ya aika wa wani yaro masoyin shi da yayi tufafi irin na shi domin nuna masa goyon baya kyautar Naira miliyan biyu da rabi N2,500,000.

Yaron yayi wannan shigar irin ta Osimhen ne a lokacin gasar gasar cin kofin AFCON na 2023 da aka gudanar a kasar Ivory Coast.

Iyalin wannan yaron yanzu ba su daina yiwa Osimhen godiya da addu’a ba tun lokacin da suka sami kuɗin.