Wasanni

Victor Osimhen: Fitar Da Iyalina Daga Talauci Shine Babbar Nasara Ta.

Olusosun karamar al’umma ce da ke kusa da wurin juji. Mutane da yawa daga cikin al’umma sukan ziyarci wurin da ake zubar da sharar don nemo kayayyaki masu mahimmanci da za su iya sayarwa don samun kuɗi.

A cewar Osimhen, da kaina, na kan je can don nemo tsofaffin takalma da zan iya amfani da su don buga ƙwallon ƙafa. Wannan al’ada ce ta gama gari kuma wani bangare ne na al’adun mu a cikin al’umma.

Baya ga haka, na kan sayar da ruwan kwalba a kan titunan Legas don in taimaka wa iyalina su samu rayuwa. Na san cewa kwallon kafa ita ce hanya daya tilo da zan fitar da iyalina daga kangin talauci, don haka na sadaukar da lokaci da kokari sosai wajen ci gaba da wannan sana’a.

Ina godiya cewa ƙwazon da nake yi ya biya, domin ya ba ni damar kyautata yanayin kuɗin iyalina. Taimakawa iyalina kubuta daga talauci shine babban nasarata. Inji Osimhen.