Nishaɗi

Turkiyya Ta Rufe Shafin Instagram A Ƙasar Ta Bisa Nuna Wariya Ga Falasɗinawa

Turkiya ta rufe hanyar shiga Instagram, a cewar hukumar sadarwar kasar, bayan da wani babban jami’in gwamnati ya yi kakkausar suka ga dandalin sada zumunta na “tace” abubuwan da ke da alaka da Hamas ko Falasɗinu.

Hukumar sadarwar ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na yanar gizo cewa, “An toshe instagram.com a wani hukunci da aka yanke a ranar 02/08/2024”, ba tare da bayyana dalilin toshewar ba.

A ranar Laraba, daraktan sadarwa na fadar shugaban kasar Turkiyya, Fahrettin Altun, ya zargi Instagram da toshe sakonnin jaje kan kisan da aka yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh.

Altun ya rubuta a kan X, yana mai cewa Instagram bai ambaci wani karya doka ba saboda shawarar da ta yanke na toshe abubuwan.

“Za mu ci gaba da kare ‘yancin fadin albarkacin baki a kan wadannan dandamali, wadanda suka nuna sau da yawa cewa suna hidima ga tsarin duniya na cin zarafi da rashin adalci ga Falasɗinu,” in ji Altun.

“Za mu tsaya tare da ‘yan uwan mu Falasdinawa a kowane yanayi kuma a kowane dandamali,” in ji shi.