Nishaɗi
Mahaifin Jarumin KannyWood, Garzali Miko Ya Rasu
Allah ya yiwa mahaifin Garzali Miko rasuwa.
Arewa Times Hausa ta samu rahoton rasuwar ne daga Abba El-Mustapha, kamar yadda ya wallafa a shafin shi na Facebook.
Haka zalika, an yi jana’izar shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garin RINGIM dake cikin jihar Jigawa.
Muna Addu’ar Allah ya Jikansa, ya gafarta masa, yasa Aljanna madaukakiya ce makomarsa.