Wasanni

Tuna-Baya: Kamaru Ta Samu Kambin Gasar Cin Kofin AFCON A 2000 Da 2002

Kamaru ta samu kambin gasar cin kofin AFCON a 2000 da 2002. Kuma a duka biyun, sun yi nasara ne a bugun daga kai sai mai tsaron gida (Penalty).

A shekara ta 2000 sun buga wasan karshe da Najeriya. Wasan dai ya zo ne da ci 2-2 a daidai lokacin da aka tashi wasan, Samuel Eto’o da Patrick Mboma ne suka ci wa Kamaru kwallo yayin da Raphael Chukwu da Austin Okocha suka ci wa Najeriya. Kamaru ta ci 4-3 a bugun fenariti.

A shekara ta 2002, sun kara da Senegal a wasan karshe, kuma bayan wasan da aka tashi babu ci, Kamaru ta ci 3-2 a bugun fanariti.

Gaba daya Kamaru ta lashe kofin AFCON guda biyar sannan kuma ita ce ta biyu bayan Masar wacce ta lashe gasar sau bakwai.