Tsundumar Matar Aure, Hafsat Tuge A Harkar Fim Ya Tayar Kura A KannyWood

Jarumar Hafsat Ismail Tuge ta zama abin tattaunawa a masana’antar Kannywood bayan da mijin ta ya yi ikirarin cewa bai ba ta izinin yin fim ba.

Kannywood ita ce kalmar da ake amfani da ita wajen yin ishara da harkar fim a arewacin Najeriya; hedikwatar ta ce a Kano.

Tuge fitacciyar jaruma ce a shirin nan na ‘Amaryar Tik Tok’, shahararren shirin gidan talabijin na Hausa.

A cewar BBC, wasan kurar ya fara ne kwanan nan lokacin da Sani Umar Gwarzo, mijin na ta, ya yi ikirarin cewa bai san ta fara wasan kwaikwayo ba.

Gwarzo ya kuma ce ya kadu bayan mutane sun sanar da shi cewa sun ga matar shi a fim.

“Lokacin da na samu kiran, na yanke shawarar yin bincike kuma na tabbatar da cewa gaskiya ne mata ta ta fara aiki ba tare da sani na ba,” in ji shi.

“Na kuma tattaro cewa tana gaya wa mutane cewa mun rabu da ita wanda hakan ya ba ta ‘yancin yin fim. Amma wannan ba gaskiya ba ne.

“A gaskiya ta kai ni kotu ta nemi a raba auren ta amma har yanzu ba a kammala shari’ar ba saboda ba ta biya kudin da kotu ta bukaci ta biya ba.”

A martanin ta, jarumar ta ce ta rabu da dan kasuwar ne kafin ta shiga Kannywood.

Tauraruwar fina-finan ta kuma yi alkawarin magance lamarin nan gaba kadan.

Da yake la’akari da cece-kucen da ya biyo baya, Ahmed Bifa, furodusan ‘Amaryar Tik Tok’, ya ce ya fito da Tuge a cikin shirin ne saboda tana da shaidar da ta dace a Kannywood.

“Takardu ta nuna cewa ‘yar kungiyar mu ce mai rijista kuma abin da nake sa rai shi ne shugabannin kungiyar ba za su yi mata rajista ba har sai sun tabbatar da cewa ba ta yi aure ba kuma ta samu izinin ‘yan uwan ta na yin fim,” inji shi. .

MUNA BINCIKE

Da yake maida jawabi shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Ismail Afakallah ya ce ana gudanar da bincike kan lamarin.

“Eh, mun sami korafi game da batun kuma mun fara aiki a kai,” in ji shi.

“Mun riga mun gayyaci jarumar (Tuge) da kuma furodusan shirin da ta fito a ciki don su bayyana a gaban mu.”

Afakallah ya ce hukumar tana da hurumin kare addini da al’adun mutanen Kano.

Ya kara da cewa hukumar za ta dauki lamarin da muhimmanci saboda nauyin shi.

Ya kara da cewa “Ya sabawa dabi’un mu da addinin mu matan aure yin fina-finai saboda aure abu ne mai tsarki a gare mu.”

Babangida Bangis, daraktan fina-finan, a baya ya ce “ka’ida ce a Kannywood” cewa ‘yan matan aure “ba za su iya fitowa a fim ba amma a bar su su zama furodusoshi.”