Wasanni

Tsohon Dan Wasan Super Eagles Na Tsakiya, Justice Christopher Ya Rasu

Tsohon dan wasan tsakiya na Najeriya, Justice Christopher ya rasu yana da shekaru 40 a duniya.

Jaridar OmaSports ta rawaito cewa ya rasu ne da safiyar Laraba a otal din sa da ke garin Jos a jihar Filato.

A shekara ta 2001 Christopher ya buga wa Super Eagles wasa kuma ya buga wasanni 11.

Yana cikin tawagar ‘yan wasan Najeriya da suka je gasar cin kofin duniya a shekarar 2002 a Koriya/Japan.

Christopher ya fara babban aikinsa a Katsina United a shekarar 1999. Bayan ya yi aiki a Sharks da Bendel Insurance, ya koma Belgium a 2001 lokacin da ya koma Royal Antwerp.

Ya kuma buga wasa a Levski Sofia da ke Bulgaria, da kulob din Trelleborgs FF na Sweden da Alania Vladikavkaz da ke Rasha da kuma Herfølge BK da ke Denmark kafin ya sanar da yin ritaya daga buga kwallo a karshen kakar wasa ta 2006/2007.

Ya koma Nasarawa United ne a watan Oktoban 2012. Ya kasance a kungiyar kwallon kafa ta Nigeria Professional Football League (NPFL) tun daga lokacin.

Advertisement