Tarihin Tsohon Kocin Kungiyar Kwallon Kafa Ta Super Eagles, Amodu Sha’aibu
Amodu Shuaibu dan wasan Najeriya ne kuma manaja wanda ya taka rawar gani a matsayin dan wasan gaba.
Ya buga wasa a Dumez da Niger Tornadoes amma rayuwarsa ba ta dade ba saboda rauni.
A matsayinsa na koci, ya horar da Super Eagles ta Najeriya sau biyar. Ya kuma horar da kungiyoyi kamar su BCC Lions, El-Kanemi Warriors, Shooting Stars da Orlando Pirates.
Amodu ya samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya sau biyu a shekara ta 2002 da kuma 2010, amma bai taba zama koci a gasar cin kofin duniya ba.
A shekara ta 2002, ya jagoranci Najeriya zuwa matsayi na uku a gasar AFCON da aka gudanar a kasar Mali sannan kuma ya ba ta damar shiga gasar cin kofin duniya ta Koriya/Japan. Amma an maye gurbinsa da Festus Onigbinde, wanda ya jagoranci kungiyar zuwa gasar cin kofin duniya.
A shekarar 2010, ya jagoranci kungiyar zuwa matsayi na uku a gasar AFCON da aka gudanar a Angola, sannan kuma ya ba ta damar shiga gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Afrika ta Kudu. Amma an maye gurbinsa da kocin Sweden Lars Lagerback, wanda ya jagoranci kungiyar zuwa gasar cin kofin duniya.
A ranar 10 ga watan Yunin 2016, Amodu ya rasu yana barci bayan ya yi korafin ciwon kirji.