Tarihin Darren Ferguson, Ɗan Alex Ferguson Tsohon Kocin Manchester United

Darren Ferguson ya taka leda a karkashin mahaifinsa Sir Alex Ferguson a Manchester United, tun yana matashi a kulob din.

Ya buga wasansa na farko a 1990 kuma lokacin da babu Bryan Robson wanda ya ji rauni, ya buga wasanni 15 na farko a United a kakar 1992/93 Premier League.

Kodayake bai fara wasan gasar ba bayan Nuwamba 1992, ya buga isassun wasanni don cancantar samun lambar yabo ta lashe gasar a karshen kakar wasa (aƙalla matches 10 a lokacin).

Saboda iyakantaccen damar da ya samu a tawagar farko, ya koma Wolverhampton Wanderers a 1994. Daga baya ya koma Wrexham inda ya shafe yawancin aikinsa, inda ya buga wasanni sama da 300.

Ya yi ritaya a shekara ta 2008 kuma a halin yanzu shine manajan kulob din Peterborough United na Championship.