Tarihin Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta “Enugu Rangers”

An kafa kungiyar ta Enugu Rangers a shekarar 1970, ita ce kungiya daya tilo da ba a taba ficewa daga gasar ta Najeriya ba.

Sun ci kofunan gasar firimiya guda 7 (Enyimba kadai da 9 ta samu karin).

Haka kuma sun lashe Kofin Gida guda shida, da na cin Kofin Nahiyar Afrika daya da kuma Super Cup na Najeriya guda daya.

A shekarar 1975, ta zama ‘yar Najeriya ta farko da ta buga wasan karshe na gasar cin kofin zakarun nahiyar Afirka ta CAF, inda ta sha kashi a hannun Hafia FC ta Guinea da ci 3-1.

Fitattun ‘yan wasan da suka taka leda a kungiyar sun hada da; Christian Chukwu, Emmanuel Okala, Emeka Onyedika, Harrison Mecha, Jay-Jay Okocha, Nana Bonsu da kuma Socràtes da Silva Nzakunibulotatimulupalatolunga dos Santos Kitcheninho.