Wasanni

Tarihi: Ɗan Kwallon Da Ya Taɓa Barar Da Bugun Finareti 3 A Wasa Ɗaya

Tsohon dan wasan Argentina Martin Palermo ne dan wasa daya tilo da ya barar bugun fanareti uku a wasa daya. Hakan ya faru ne a wasan Copa America a shekarar 1999 tsakanin Argentina da Colombia.

Fenariti na farko ya sake dawo da bugun daga kai sai mai tsaron gida Miguel Calero. Colombia ta yi nasara a kan wasan da ci 3-0.

A matakin kulob, Palermo ya taka leda ne a Boca Juniors kuma shi ne wanda ya fi kowa zura kwallaye a kulob din da jimillar kwallaye 236.

A halin yanzu shi ne kocin Aldosivi, wani kulob da ke Argentina.

Advertisement