Sen Vs Egypt: Wata Mata Ta Danganta Nasarar Senegal Da Karamar Inyass

A yau ne 6 ga watan 1, na shekarar 2022 aka kawo karshen gasar cin kofin kwallon kafar Nahiyar Afirka na shekarar 2021 wanda aka jinkirta har zuwa 2022 saboda annobar cutar Covid-19.

A takaice ƙasar Senegal ita ce ta lashe wannan kofin na 2021 bayan ta doke ƙasar Masar a bugun daga kai sai mai tsaron gida, wato bugun finareti da aka samu saboda lokacin wasan ya kammala kuma babu wanda ya zura kwallo a raga.

Senegal ta zura kwallaye 4 a ragar Masar, yayin da Masar ta samu damar zura 2 a ragar Senegal kacal lokacin bugun finaretin.

Jim kadan da lashe gasar da Senegal tayi, sashen Hausa na BBC ya wallafa labarin nasarar ta Senegal, mintoci kadan da sakin labarin a Facebook sai wata mata ta bayyana cewa nasarar ta yan wasan Senegal ba komai ba illa karamar Shehu Inyass ce ba su wannan damar ta ɗaga kofin na 2021 da aka kammala bugawa a ƙasa Kamaru.

Ga abinda matar ta wallafa a kasa;