Al'umma

Muna Da Adadin Aljanu Biliyan 4 Da Suka Shiga Tijjaniyya – Dahiru Bauchi

Babban shehin malamin darikar Tijjaniyya a Najeriya Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya bayyana cewa sun samu kimanin Aljanu miliyan dubu hudu (biliyan 4) da suka shiga cikin darikar shi ta Tijjaniyya.

Malamin wanda ga dukkan alamu yayi wannan bayanin ne lokacin da yake yin wa’azi a wurin tafsirin Alqur’ani maigirma yace, kamar yanda shedanun aljanu suke suke tare da masoyan su, haka zalika muminan aljanu suke tare muminan mutane.