Mohammed: Shahararren Ɗan Dambe Na Duniya

A shekarar 1980, fitaccen dan damben nan Mohamed Ali ya riga ya kamu da cutar Parkinson, kuma yana da shekaru kusan 40 a duniya, amma ya amince ya buga wasan karshe da Larry Holmes (wanda ya san halin lafiyar Ali) saboda bukatarsa ​​ta samun kudi don biyan wasu kudade, bashin haraji da kuma tabbatar da ritayarsa.

Kamar yadda aka yi tsammani, Ali yayi rashin nasara a wasan, amma sai wani yaro dan shekara 14 ya tunkare shi bayan an gama wasan, yaron ya ce wa Ali, zan rama maka rashin nasarar ka.

Shekaru 8 bayan haka, a cikin shekara ta 1988 wannan yaron ya lallasa Larry Holmes kuma ya zama sabon zakaran duniya.

Bayan kammala wasan sai ya ziyarci Mohamed Ali ya kuma tunatar da shi alƙawarin yana mai cewa: A yau na cika alkawari da na yi maka zakara.

Sunan yaron Mike Tyson.