Matsayar José Mourinho Kan Harkar Kwallon Kafa A Afrika

José Mourinho – “Ina son duniya ta gane cewa Afirka tana daidai da kowa. ‘Yan Afirka ba a bar su baya ba cikin hazaka. Suna da hazakar lashe kowace gasar kwallon kafa, sai dai mafi yawan ’yan wasan kasashen Afrika sun warwatsu a duniya suna buga wasa a wasu kasashe maimakon kasashen su na asali.

Na san ba zan yi farin jini ba ga wasu kungiyoyi kuma mutane ba kan wadannan kalami ba, amma ya kamata kungiyar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta yi adalci ta hanyar kin barin ‘yan wasa su wakilci wasu kasashen da ba na su a wasannin cin kofana, domin hakan zai sa gasar FIFA ta kara zama mai armashi ba tare da bangaranci ba.” Inji José Mourinho.