Matashin Ɗalibin Jami’ar Najeriya Ya Kera Ƙaramin Jirgin Sama

Wani matashi dan Najeriya, Hafizh Husssaini, ya samu karbuwa a kafafen yada labarai ta hanyar fasahar shi ta lantarki yayin da ya kera wani karamin jirgin sama wanda zai iya tashi a matsayin maras matuki.

A wani hoton bidiyo da gidan talabijin na YAY TV ya wallafa, ya bayyana cewa matashin wanda dalibin jami’ar jihar Kano yana burin wata rana ya zama matukin jirgin sama.