Matashi Yayi Tattaki Kan Keke Daga Benue Don Kai Wa Ahmed Musa Ziyara

Shahararren dan kwallon Najeriya, kuma kaftin kungiyar kwallon Super Eagles, Ahmed Musa ya wallafa a shafin shi na sada zumunta cewa wani matashi yayi ya kawo masa ziyara bisa keke tun daga jihar Benue.

Kamar yadda zaku gani a cikin hotuna, matashin ya haɗu da Ahmed Musa inda suka gaisa da juna da kuma nuna godiya ga irin soyayyar da wannan matashin ya nuna masa.

Ga abin da Ahmed Musa ya wallafa a shafin shi:

Babbar jinjina ga wannan hazikin matashi wanda ya yi tukin keke daga jihar Benue don kawai ya ziyarce ni! sadaukarwar ku da goyon bayan ku na nufin duniya a gare ni!