Gola Ɗaya Tilo Da Ya Taɓa Lashe Gasar UEFA Champions League Da Kulob Daba-Daban

Edwin van der Sar ne mai tsaron gida daya tilo da ya lashe gasar zakarun Turai da kungiyoyi daban-daban (Ajax a 1995 da Man United a 2008).

Shi ne kuma dan wasa mafi tsufa da ya lashe gasar Premier, bayan da ya yi hakan a shekarar 2011 yana da shekaru 40 da kwanaki 205.