Labarai

Mahaifiyar Tsohon Shugaban Najeriya, Umar Musa Yar’adua Ta Rasu

Rahotanni sun bayyana cewa ta rasu ne a asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya dake Katsina a ranar Litinin bayan gajeriyar rashin lafiya.

Tana da shekaru 102.

Dada ta kasance mahaifiyar marigayi Shehu Musa Yar’adua da kuma Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua, shugaban kwamitin majalisar dattawa a kan sojoji a yanzu.

Umaru Musa ‘Yar’aduwa ya zama shugaban kasar Najeriya daga shekarar 2007 har zuwa rasuwarsa a watan Mayun 2010.

Ya taba rike mukamin gwamnan jihar Katsina daga 1999 zuwa 2007.