Labarin Wani Mahajjaci Da Ya Shiga Dakin Ajiyar Gawa Don Hutu

A yan shekarun baya, an samu mahajjaci ɗan ƙasar Sudan da yaje wurin hawan Arfa kamar yadda sauran mahajjata ke tafiya, amma saboda tsananin zafin rana da na cinkoson jama’a da aka yi fama da shi a wannan lokacin, sai wannan mahajjacin yayi gumi, kuma ga zafi na damun shi sosai.

Haka zalika, sai aka yi sa’a a kusa ga wannan bawan Allah akwai wani abin sanyaya daki (AC) a jikin wani hango na wani dan ɗaki, kuma sai yaji sanyi na ta hurowa daga cikin dakin, sai dai kuma akwai wani mai tsaro a wurin (Askar) nan a bakin ɗakin.

Bayan wani ɗan lokaci kadan, sai wannan mahajjacin ya matso kusa ga, cikin sa’a ya shammaci wannan mai tsaron ya shige ciki bai lura ba.

Dattijon yana shiga ya ci karo da wasu Alhazzan duk suna barci bai, naka bai tsaya wata-wata ba shi ma ya zube don shan sanyi, nan da-nan barci ya kwashe shi.

Bayan ya farka daga barci, sai ya fito waje, yana fitowa suka haɗa ido da wannan mai tsaron dakin sai yaga ya zuba a guje, wannan mahajjacin cike da mamakin abinda yasa wannan mai tsoron ke yiwa gudu, yana juyawa ya duba dakin shi ma a firgice ya zuba da gudu.

Ashe abin da ke rubuce a saman dakin shi ne (ثلاجة موات). Ma’ana (Dakin Aje Gawa).