Wasanni

Kyautar Gwarzon Ɗan Wasan Kwallon Kafa Afirka Na 2008, Mai Cike Da Cece-Kuce

Emmanuel Adebayor na Togo ne ya zo na daya, sai Mohammed Aboutrika na Masar ya zo na biyu sai kuma Michael Essien na Ghana ya zo na uku.

A wannan shekarar, Aboutrika ya lashe gasar AFCON tare da Masar. Ya kuma lashe gasar Premier ta Masar da Super Cup na Masar da kuma CAF Champions League tare da Al Ahly.

Bugu da kari, ya zama gwarzon CAF na shekara, ya zama kungiyar mafarkin AFCON a 2008, ya zama gwarzon dan wasa a wasan karshe na AFCON kuma ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afrika na BBC.

A daya bangaren kuma, Adebayor bai lashe kofi ko lambar yabo ba a wannan shekarar ba. Ya zo na uku da Arsenal a gasar Premier.

Magoya bayan shi da dama sun yi imanin dalilin da yasa Aboutrika bai lashe kyautar ba shi ne saboda baya buga wasa a Turai.