Kwallon Kafa: Bugun Kunamar René Higuita

René Higuita sunan ne da duk masoya kwallon kafa suke ji ko suka taba ji a wani lokaci a rayuwar ta fannin wasannin kwallon kafa. Hatta matasa ‘yan wasan sun san sunan shahararren mai tsaron gidan Colombia (goalkeeper).

Mafi yawan masoya kwallon kafa sun san René Higuita me duk saboda fitaccen bugun kunama da ya yiwa kasar Ingila a shekarar 1995, wannan bugun zai ci gaba da kasancewa a tarihin kwallon kafa har abada.

A yayin wannan wasan sada zumuncin, dan kasar Colombia ya tare kwallon da dan kasar Ingila Jamie Redknapp ya bugo zuwa ragar Colombia ta hanyar tsalle-tsalle sannan ya buga kwallon da diddiginsa na kafafu biyu a lokaci guda.