Kulob Da Ya Saka Yan Wasa 11 Daga Kasashe Daban-Daban A Wasa Ɗaya A UEFA

Arsenal ta zama kungiya ta farko a tarihin gasar zakarun Turai da ta fitar da ‘yan wasa goma sha daya daga kasashe daban-daban a lokaci guda, a wasan da suka doke Hamburger SV da ci 2-1 a ranar 13 ga Satumban 2006.

‘Yan wasan goma sha daya sune:

 • Jens Lehmann (Jamus)
 • Emmanuel Eboue (Ivory Coast)
 • Johan Djourou (Switzerland)
 • Justin Hoyte (Ingila)
 • William Gallas (Faransa)
 • Tomas Rosicky (Jamhuriyar Czech)
 • Gilberto Silva (Brazil)
 • Cesc Fabregas (Spain)
 • Alexandre Hleb (Belarus)
 • Emmanuel Adebayor (Togo)
 • Robin van Persie (Netherland)