Kotu Ta Bayar Da Umarni Kamo Mawaki Ado Gwanjo Bisa Wakokin Batsa

Wata kotu dake babban birnin jihar Kano, Arewacin Najeriya ta bayar umarnin kamo mawaki Ado Gwanja bisa wakoki alfasha da iya lalata tarbiyyar ya’yan musulmai.

Kotun ta bayyana cewa Ado Gwanjo da wasu mutane daban suna amfani d wakoki da sauran wasu hanyoyi alfasha wajen lalata tarbiyar al’umma kamar yadda kotun ta ƙarf korafi da wasu masu kishin al’umma.

Wannan umarnin na zuwa ne bayan gurfanar da yan TikTok mata Murja Kunya da Ramlat Princess a gaban kotu kan dabi’unsu na yaɗa alfasha a cikin al’umma.