Wasanni
Kocin Farko Wanda Ba Ɗan Italiya Ba Da Ya Taɓa Lashe Gasar “Serie A” Tun Ƙarni Na 21
Jose Mourinho shi ne kadai kocin da ba dan Italiya ba da ya taɓa lashe gasar Seria A tun karni na 21.
Kocin dan kasar Portugal ya lashe gasar Seria A sau biyu a jere tare da Inter kafin ya tafi Real Madrid a shekara ta 2010.
Koci na karshe wanda ba dan Italiya ba da ya lashe gasar Seria A kafin Mourinho shine Sven-Goran Eriksson (Sweden) tare da Lazio a 1999-2000.