Wasanni

Ko Ka San Yan Wasan AC Milan Da Suka Buga Gasar UCL Ta 2005 Duk Sun Yi Ritaya?

An buga wasan karshe na UCL a shekarar 2005 tsakanin Liverpool da AC Milan.

Duk ‘yan wasan AC Milan da ke wannan tawagar sun yi ritaya. Duk da haka, uku daga cikin ‘yan wasan Liverpool suna ci gaba da aiki.

Milan Baros mai shekaru 40 a halin yanzu yana taka leda a FK Vigantice.

Djibril Cisse mai shekaru 40 a duniya ya buga wa Panathinaikos Chicago wasa.

Scott Carson mai shekaru 36 a yanzu yana taka leda a Manchester City.