Wasanni
Ko Ka San Celestine Babayaro Shi Ne Ɗan Najeriya Na Farko Da Ya Fara Bugawa Chelsea Wasa?
Celestine Babayaro ya zama dan Najeriya na farko da ya fara bugawa Chelsea wasa a lokacin da ya koma kulob din na Landan a watan Afrilun 1997, yana da shekaru 18 a duniya, kan kudi fam miliyan 2.25, tarihin da kulob din ya biya ga wani matashi a lokacin.
Ya buga wa Chelsea wasanni sama da 200, inda ya lashe kofin gasar cin kofin UEFA Cup, UEFA Super Cup, FA Cup da FA Charity Shield.
Duk da haka, ya yi fama da wasa lokacin da Mourinho ya karbi ragamar kungiyar a shekara ta 2004, saboda kocin na Portugal ya fi son ya buga Wayne Bridge a wannan matsayi.
Babayaro ya bar Chelsea zuwa Newcastle a watan Janairun 2005.