Kasashen Afrika 2 Da Suka Fara Buga Ƙwallo A Gasar Cin Kofin Duniya

Kasar Masar ta zama kasa ta farko a Afirka da ta fara buga gasar cin kofin duniya a lokacin da ta halarci gasar a shekarar 1934.

Ba a buga wasannin rukuni-rukuni a waccan gasar ba, saboda an fara ne da matakin bugun daga kai sai mai tsaron gida. Masar ta sha kashi a hannun Hungary da ci 4-2 a zagaye na 16.

A shekarar 1970, Morocco ta zama kasa ta biyu a Afirka da ta taka leda a gasar cin kofin duniya yayin da Zaire (yanzu DR Congo) ta zama ta uku a shekarar 1974.