Wasanni

Real Madrid Ta Fara Kare Kambun Liga Bayan Kunnen Doki Da Mallocra

Real Madrid ta tashi kunnen doki 1-1 da Mallorca a wasan farko na gasar La Liga a ranar Lahadi.

Kylian Mbappe ya fara buga gasar La Liga a wasan amma ya kasa taimakawa kungiyarsa samun nasara.

Ku tuna cewa dan wasan na Faransa ya zura kwallo a ragar kungiyar a wasan da suka doke Atalanta da ci 2-0 a gasar cin kofin Uefa a ranar Laraba.

Amma kokarin da ya yi a kan Mallorca duk ya ci tura domin mai tsaron golar gida ne ya hana shi zura kwallo a bugun shi.

Rodrygo ya zura kwallo a ragar Mallocra bayan wani fasin daga Vinicius Junior wanda hakan ya baiwa kungiyar Carlo Ancelotti jagora a wasan.

Sai dai Vedat Muriqi ya rama kwallon da kai daga bugun daga cross na Dani Rodriguez, kuma masu masaukin baki sun samu maki daya a karawar da suka yi da zakarun.

Madrid ta kammala wasan da ‘yan wasa 10 yayin da aka bai wa dan wasan bayanta Ferland Mendy jan kati a lokacin ƙarshe sakamakon keta ga Murigi.