Hisbah Ta Cafke Ramlat Princess Kan Bidiyon Badala

Dakarun hukumar Hisbah sun nasarar cafke wata matashiya mai suna Ramlat Princess bisa wasu kalaman alfasha da ta yi cikin bidiyo a shafukan sada zumunta.

Matashiyar dai ta tallata kanta a cikin bidiyon inda take cewa duk namijin da zai aure ta dole sai ya auro mata wata macen daban da zasu dinga lalata da ita.