Golan Farko Da Aka Taɓa Cirewa A Wasan Karshe Ta UCL

Golan Arsenal Jens Lehmann ya zama dan wasa na farko da aka bai wa jan kati a wasan karshe na gasar UCL bayan da ya yi wa Samuel Eto’o na Barcelona keta a minti na 18 a shekara ta 2006.

‘Yan wasa 10 Arsenal sun fafata sosai a minti na 37 da fara tamaula ta hannun Sol Campbell, kafin daga bisani Eto’o ya ramawa Barcelona a minti na 76 sannan Juliano Beleti ya ci kwallon a minti na 80.

Didier Drogba (a cikin 2008) da Juan Cuadrado (a cikin 2017) sun zama na biyu da na uku da aka ba su jan kati.