Kimiyya
Garrett Augustus Morgan: Masanin Kimiyyar Afirka
Garrett Augustus Morgan, Sr. wanda aka haifa a 3/4/1877, kuma ya rayu har zuwa Yuli 27, 1963, ɗan Afirka ne mai kirkire-kirkire, ɗan kasuwa, kuma shugaban al’umma.
Fitattun abubuwan ƙirƙira nasa sune hasken fitila masu kula da jirga-jirgar ababen hawa, wanda shine siginar hanya uku ta farko da abin rufe fuska na iskar gas da aka yi amfani da shi musamman a cikin wani bala’i na ceton rayuka 1916.