Wasanni
Fitattun Ƴan Wasan Ƙwallon Ƙafa 10 Daga Arewacin Najeriya
Arewacin Najeriya, yanki ne da ya shahara da tarin al’adun gargajiya da kuma sha’awar wasa mai kayatarwa, ya samar da kwararrun ‘yan wasan kwallon kafa da suka yi fice a fagen wasan kwallon kafa.
Tun daga titunan Kano har zuwa filayen wasan Kaduna, yankin na da dadadden tarihi wajen raya kwararrun ‘yan wasan kwallon kafa da suka yi ta kai ruwa rana a cikin gida da waje. A wannan makala, Arewa Times Hausa ta lissafa fitattun ‘yan wasan kwallon kafa guda 10 da suka fito daga Arewacin Najeriya.
Yan wasan sune; Ahmad Musa, Jamilu Collins, Moses Simon, Umar Sadiq, Shehu Abdullahi, Sanusi Ibrahim, Zaidu Sanusi, Ibrahim Rabi’u da Alhassan Yusuf.