Erling Haaland: Ɗan Wasan Da Ya Taɓa Cin Ƙwallaye 9 A Wasa Ɗaya

Ka tuna lokacin da Erling Haaland ya ci kwallaye tara a wasa daya tilo?

A gasar cin kofin duniya na U20 na 2019 da aka gudanar a Poland, Norway ta doke Honduras 12-0 a karawar da suka yi a matakin rukuni kuma Haaland ya zura kwallaye uku sau uku a raga.

Sai dai har yanzu Norway ta zama ta uku a rukunin, bayan da ta yi rashin nasara a wasanni biyu da ta yi.