Al'umma
Darasi 14 Na Rayuwa
- Kada ka ba yan uwan ka rancen kuɗi. Ka ba su kyauta.
- Kada ka bada hannu wajen gaisuwa yayin da kake a zaune.
- A daina gaya wa mutane abubuwa fiye da yadda suke bukata.
- Kada ka taɓa cinye abinci na ƙarshe da ba kai ka saya ba.
- Kada ka jefa abokinka a cikin damuwa don burge wani.
- Kada ka taba kushe girkin gidan da kake baƙunci.
- Kada a yi fitsari a kusa da wani mutum.
- Kada ka fitar da wayar ka yayin da kuke zance.
- Kada ka taɓa yin la’akari da aikin da ba ka yi ba.
- Kada ka yiwa abokinka dariya a gaban ‘ya’yansa.
- Kada ka bari gaggawa ta rinjaye ka.
- Kada ka taba rokon soyayya.
- Sanya tufafi da kyau ko da wane lokaci ne.
- Kada ka taɓa cutar mutum idan yana cikin matsala.