Wasanni
Cha Bum Kun: Tsohon Ɗan Wasan Koriya-Ta-Kudu da Ya Zura Ƙwalleye 58 Raga A Wasanni 136
Cha Bum-kun dan wasan kwallon kafar Koriya ta Kudu ne mai ritaya da ake yi wa kallon daya daga cikin manyan yan wasan Asiya da aka taba yi.
Shi ne dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a raga a Koriya ta Kudu da kwallaye 58 a wasanni 136 da ya buga. Haka kuma shi ne dan wasa mafi karancin shekaru da ya taba buga wasa 100 a duniya a shekaru 24 da kwanaki 139.
A cikin 1972, ya zama ƙaramin ɗan wasa da aka kira zuwa tawagar Koriya ta Kudu.
Ɗansa Cha Du-ri, wanda shi ma ya yi ritaya, shi ne ɗan wasan Koriya na farko da aka haifa a wajen Koriya (an haife shi a Frankfurt, Jamus) da ya taka leda a gasar cin kofin duniya ta FIFA.
Dukkan su uba da dan sun taka leda a Bayer Leverkusen da Eintracht Frankfurt.