Babu Talauci A Duniya Sai In Wani Ne Ya Ƙirƙire Shi – Maradona
Sa’ad da nake da ƙuruciya, na sha fama da talauci sosai yayin da wasu yara kuma suke yin taƙama da ɗimbin dukiyar dangin su!
Ina son kwallon kafa domin bata taba sa ni talauci ba; lokacin da muka fara wasa, hazaka ita ce muhimmin abu.
Ban taɓa jin haushin masu kuɗi ba, amma a gaskiya, ba daidai ba ne. Abin da na saba gaya wa kaina kenan!
Yawancin yaran masu arziki sun girma suna da komai.
Amma duk yadda kake da wadata, ba za ka iya siyan hazaka ba. Don haka a lokacin, kowa ya kasance yana cewa:
“Shin Maradona ba shi da abin da ya fi cancanta?”
Tabbas, babu sharhi.
Wata rana, na je fadar Vatican na ga rufin cocin da aka zana da zinariya, kuma Paparoma yana bada jawabi game da tallafa wa talakawa.
La’ananne. sayar da silin na zinaren!
Na tabbata babu talauci a duniya sai dai idan wani ne ya kirkire shi.
– Diego Armando Maradona