Auren Laylah Ali Othman

Laylah Ali Othman, wata shahararriyar ‘yar kasuwa kuma mai mujallar L Magazine ta daura aurenta da mijinta, Rt Hon Yusuf Adamu Gagdi, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Pankshin, Kanke da Kanam, a ranar Juma’a.

Shafin na BBC Hausa ne ya sanar da hakan a shafinsu na Facebook tare da yada wasu hotunan ma’auratan cikin farin ciki.