An Shigo Da Bulun Kati (Blue Card) A Dokokin Kwallon Kafa

Sabuwar doka a ƙwallon ƙafa: katin bulu! 🟦

Za a yi amfani da shi wajen fitar da dan wasa daga filin wasa na tsawon mintuna 10 idan ya aikata laifin da zai hana kai harin da ake ganin yana da hadari ko kuma ya nuna adawa da alkalancin alkalin wasa.

Katin bulu + katin dorowa zai haifar da katin ja. 🟦+🟨=🟥

Bulun kati biyu zai haifar da korar dan wasa. 🟦+🟦=🟥

Za a gudanar da matakin gwaji na farko, watakila a gasar cin kofin FA. Ba za a fara amfani da shi a manyan gasar kwallon kafa ba.