Labarai

An Samu Lu’ulu’u Na Biyu Mafi Girma A Duniya A Botswana

An gano lu’u-lu’u mai girman carat 2,492 – na biyu mafi girma a duniya – a kasar Botswana, in ji kamfanin hakar ma’adinai na Kanada wanda ya gano dutsen.

An gano lu’u-lu’u a ma’adinan Karowe Diamond dake arewa maso gabashin Botswana ta hanyar amfani da fasahar X-ray, in ji kamfanin na Lucara Diamond Corp a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Lucara bai bayar da wata kima ba ko kuma ya ambaci ingancinsa ba. Amma ta fuskar carats, dutsen ya kasance na biyu bayan lu’ulu’u mai awon 3,016 da aka gano a Afirka ta Kudu a 1905.

Shugaban Lucara William Lamb ya ce “Muna matukar farin ciki game da dawo da wannan lu’u-lu’u mai girman carat 2,492.”

Hotunan da kamfanin ya fitar sun nuna cewa lu’u-lu’u yana da girma kamar tafin hannu.

Wannan binciken ya kasance “daya daga cikin mafi girman lu’ulu’u mafi girma da aka gano” kuma an gano shi ta hanyar amfani da fasahar X-ray na kamfanin Mega Diamond Recovery da aka sanya a cikin shekarar 2017 don ganowa da adana manyan lu’u-lu’u masu daraja, in ji sanarwar.

An nuna wa shugaban kasar Botswana Mokgweetsi Masisi katafaren dutsen daga baya a ranar Alhamis. Gwamnatinsa ta ce ita ce ta biyu mafi girma a duniya.