Ahmed Hassan: Kwararren Ɗan Kwallon Kasar Masar

Ahmed Hassan shi ne dan wasan da ya fi kowa taka leda a Masar (ya halarci wasanni 184) kuma shi ne na hudu a tarihin kwallon kafa a duniya.

Haka kuma shi ne dan wasa na 5 da ya fi zura kwallaye a Masar da kwallaye 33, bayan Mohamed Aboutrika (38), Hassan El Shazly (42), Mohamed Salah (51) da Hossam Hassan (68).

Hassan shi ne dan wasa daya tilo da aka baiwa kyautar gwarzon dan wasan AFCON a gasa daban-daban guda biyu (AFCON 2006 da AFCON 2010).

Tare da Rigobert Song na Kamaru, yana daya daga cikin ‘yan wasa biyu da suka taka leda a gasar AFCON daban-daban takwas.

Tare da dan kasar Essam El Hadary, yana rike da tarihin mafi yawan kofunan AFCON da aka ci a matsayin dan wasa (4)- 1998, 2006, 2008, 2010.

Hassan ya yi ritaya daga buga kwallo a watan Disamba 2013.