Wasanni
AFCON: Abu 5 Da Baku Sani Ba A Tarihin Gasar Ba
1. Charles Gyamfi na Ghana (1963, 1965, 1982) shi ne koci na farko da ya lashe gasar ta AFCON har sau uku.
2. Hassan Shehata na Masar (2006, 2008, 2010) shine koci daya tilo da ya lashe gasar AFCON sau uku a jere.
3. Mahmoud El-Gohary na Masar shi ne mutum na farko da ya lashe gasar AFCON a matsayin dan wasa (1959) kuma koci (1998).
4. Stephen Keshi na Najeriya shi ne na biyu da ya ci ta a matsayin dan wasa (1994) kuma koci (2013).
5. Herve Renard dan kasar Faransa ne kadai kocin da ya lashe gasar AFCON da kungiyoyi daban-daban (Zambia a shekarar 2012 da kuma Ivory Coast a 2015).