Wasanni
Abinda Yasa Rogerio Ceni Ya Zama Golan Da Ya Fi Zura Ƙwallo Raga A Duniya
Rogerio Ceni shi ne golan da ya fi kowane golan duniya zura kwallo a raga da jimillar kwallaye 131.
Ya shafe shekaru 22 a kulob din Sao Paulo na Brazil, kuma ya kasance mai bugun fanareti.
A matakin kasa da kasa, an kira shi sau 17 don Brazil. Ya kasance cikin tawagar da ta lashe gasar cin kofin duniya ta FIFA a shekarar 1997 da kuma gasar cin kofin duniya a shekarar 2002.
Ya kuma taka leda a gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2006.
A halin yanzu Ceni shine manajan Sao Paulo.