Abinda Ya Kamata Ku Sani Game Da Gasar Cin Kofin Afrika, AFCON 2023

A ranar 13 ga watan Junairu ne ake sa ran za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON 2023, wadda hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta shirya.

Gasar za ta baje kolin manyan taurarin kwallon kafa na nahiyar, wadanda tuni suka taka rawar gani a kungiyoyin su da kuma gasar cin kofin duniya ta Qatar 2022.

Kungiyoyi biyar da suka halarci gasar cin kofin duniya na baya-bayan nan a Qatar za su halarci gasar AFCON 2023, inda Morocco, wacce ta kai wasan kusa da karshe a gasar cin kofin duniya, ita ce ke kan gaba wajen lashe gasar.

Ga wasu muhimman bayanai game da gasar AFCON mai zuwa:

Ƙungiyoyin da suka cancanta

  • Rukunin A – Ivory Coast, Nigeria, Equatorial Guinea, da Guinea-Bissau
  • Rukunin B – Masar, Ghana, Cape Verde, da Mozambique
  • Rukunin C – Senegal, Kamaru, Guinea, da Gambia
  • Rukunin D – Algeria, Burkina Faso, Mauritania, da Angola
  • Rukunin E – Tunisia, Mali, Afirka ta Kudu, da Namibiya
  • Rukunin F – Morocco, DR Congo, Zambia, da Tanzania